Barasa ta halaka mutane 35 a Indiya
November 7, 2021Talla
Yanzu haka dai 'yan sanda a kasar ta Indiya sun kaddamar da bincike, har ma an kai ga kama mutane 19 da ake zargi da hannu a lamarin shan barasar da ya yi sandin rayukan mutane da dama, an kuma dakatar da 'yan sanda tara daga aiki.
Hukumomi a Indiya sun ce akalla mutane 1,000 na mutuwa duk shekara yawanci daga yankuna marasa galihu sakamakon shan barasar gargajiya. Ko a shekarar 1992 mutane 200 sun mutu a jihar Odisha da ke gabashin kasar ta Indiya, wasu 180 sun mace a yammacin Bengal a 2011.
Dama dai gwamnatin jihar da lamarin ya faru ta haramta sha da sayer da barasa tun gabanin zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a 2016.