SiyasaAfirka
Senegal: A hukumance an tabbatar da zababben shugaban kasa
March 30, 2024Talla
Kotun tsarin mulki a Senegal, ta tabbatar da jagoran adawar kasar Bassirou Diomaye Faye a matsayin zababben shugaban kasa.
A cewar kotun Diomaye Faye ya lashe zaben da kashi 54% na kuri'un da aka kada a zaben karshen makon jiya.
Tsohon firaminitan kasar ta Senegal, Amadou Ba shi ne mutumin da ya zo na biyu a zaben a cewar kotun da kashi 36%.
Wannan matsayi na kotu dai ya kore rade-raden da wasu 'yan kasar ke yi game da yiwuwar zuwa zagaye na biyu tun da farko.
An dai sa ido sosai a kan zaben na Senegal ganin yadda kasar ta fama da darigizar siyasa kusan ta shekara guda.
A bara ne dai shiru din da Shugaba Macky Sall ya yi game ko zai tsaya takara a karo na uku ya haddasa bore a Senegal din.