1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauye-sauye a Bankin raya kasashen Afirka

Salissou BoukariMay 26, 2016

A wannan makon ne Bankin raya kasashen Afrika, AFDB, ke gudanar da taronsa na shekara-shekara a birnin Lusaka na kasar Zambiya, domin samar da sabbin dabarun bunkasa nahiyar.

https://p.dw.com/p/1IuzS
Akinwumi Adesina, neuer Präsident der Afrikanischen Entwicklungsbank
Akinwumi Adesina shugaban bankin raya kasashen Afirka na AFDB, ko BADHoto: AFP/Getty Images/S. Kambou

Shi dai bankin raya kasashen na Afirka na da manya-manya buri guda biya da ya sa ma gaba, da suka hada da samar da isheshiyar wutar lantarki ga kasashen na Afirka, samar da abinci, da manyan masana'antu, saka kasashen na Afirka cikin sahun kasashen duniya, da kuma batun inganta rayuwar al'ummomin kasashen na Afirka inda a cewar shugaban wannan banki Mista Akinwumi Adesina wanda tsohon ministan harkokin noma ne na Tarayyar Najeriya, a halin yanzu dai sun kammala aikin tsara wannan manyan burori guda biyar da za su dukufa nan gaba a kansu idan har babban taron da ya kumshi shugabannin kasashen da na gwamnatocin na Afirka ya amince da wannan tsari.

Shugaba Bankin raya kasashen na Afirka Adesina ya ce daga cikin manyan ayyukan guda biyar da suka sama gaba, za su dauki guda biyu a matsayin ayyuka na gaggawa wanda hukumar za ta sa a gaba kuma wadannan ayyuka sun hada da batun samar da makamashi ga kasashen na Afirka, da kuma inganta rayuwar al'umma musamman ma matasa ta hanyar samar musu ayyukan yi wanda hakan zai ba su damar walwala da inganta rayuwa. Kimanin jihohi kamar guda shida ne dai a Tarayyar Najeriya ke cin gajiyar tallafin da wannan banki ke bayar wa a fannoni daban-daban musamman na noma.