Saudiyya da Iran sun sasanta
April 6, 2023Talla
Zaman da China ta jagoranci manyan jami'an diplomasiyyar Iran da Saudi Arabia wadanda suka kwashe shekaru suna rikici da juna a yankin Gabas ta Tsakiya sun amince da jingine banbancin da ke tsakaninsu a wani mataki na kawo karshen zaman tankiya da suke yi.
A wani faifan bidiyo da kafar yada labaran Iran ta wallafa ya nuna yarima Faisal bin farhan na Saudiyya da takwaransa na Iran Hossein Amirabdullahian sun yi musabaha.
Kazalika kasashen biyu za su maida dangantakar diplomasiyya da ma bude ofisoshin jakadancinsu da maida hada-hadar jiragen sama gami da bude kofofin ci gaba da ziyara a tsakaninsu.