Sata na kan gaba a zaɓen shugaban Zambiya
September 21, 2011Alƙaluman farko na zaɓen shugaban ƙasar Zambiya sun nunar da cewar ɗan takaran jam'iyun adawa Michael Sata na gaban shugaba me barin gado Rupiah Banda da yawan ƙuri'u. Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana sakamakon mazaɓu 22 daga cikin 150 da ƙasar ta ƙunsa, a inda ta ce ya zuwa yanzu Sata ya lashe kashi 44,5% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Rupiah Banda da ke kan karaga ya samu kashi 33% na ƙuri'un. Bisa ga dokokin ƙasar ta zambiya dai, ranar alhamis ne idan Allah ya kaimu ya a bayar da cikakken sakamakon zaɓen da ya gudana ranar talata.
Sai dai an sake fiskantar wani tashin hankali a Solwezi da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar bayan da mazauna garin suka zargi jami'ian hukumar zaɓe da nuna son kai a lokacin da suke gudanar da aikinsu. Dama ma dai a ranar zaɓe ma an fiskanci tashe tashen hankula a birnin Lusaka sakamakon jinkiri da aka samu wajen fara kaɗa ƙuri'a. sai dai Harison Ntundu, wani ɗan jarida da ya shaidar da zaɓen ya ce wannan rikici ya gurgatan aikin su na farautar labarai.
"Akwai yankuna da ba mu samu damar shiga ba saboda an ta harbe harben bindigogi, kana an katse zirga zirgan motoci. Mun so mu yi hayar mota domin ta kewaya da mu wasu runfunan zaɓe, amma kuma fargaba da tsoro suka hana direbobi kai mu inda muka bukata. Amma mun samu bayanai da ke nuna cewar 'yan adawa sun mamaye wasu runfuna tare da lallasa wasu mutane."
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita:Yahouza Sadissou Madobi