1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

sarrafa shara zuwa makamashi a Gabon

Nura Datti/GATDecember 2, 2015

Firmin Makaya ya bullo da wata dabara ta amfani da shara da kuma tarkace wajen sake sarrafasu don tsaftace muhalli da kansa da kuma dogaro da kai a kasar Gabon

https://p.dw.com/p/1HG1l
Pakistan Umwelt
Hoto: picture-alliance/AA

Garin Lambarene da ke cikin kasar Gabon ya kasance yana fama da taruwar shara da kuma tarkace a ko ina, sai dai wani matashi Firmin Makaya ya bullo da wata dabara ta amfani da sharar da kuma tarkace wajen sake sarrafa su don tsaftace muhallin kansa da kuma dogaro da kai,

Firman Makaya, ga a al'ada yana ziyartar babbar kasuwar Lambarene tare da tattaro dagwalo. Shugaban kanfanin ya yi wa tashar DW karin bayani kan anfanin hakan.

" A kan yi rashin sa'a sai ka ga mutane na jefar da shara ko kuma tarkace a kan tituna barkatai, ba tare da sun yi la'akari da cewar za'a iya sake sarrafasu ba, don haka muke kokarin wayar musu da kai kan anfanin da hakan yake da shi, duk cewar zubar sharar barkatai kan haifar da cututtuka".

Abfallhaufen auf dem Oktoberfest 2014
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Ribnitzky

Shekaru da daman gaske garin Lambarene na fuskantar kalubalen shara duk da cewar akwai hukumar da ke kula da harkokin tsaftace muhalli amma fa a baki ne kawai, wanda kuma hakan ne ya karfafawa Makaya gwiwar samar da cibiyar amsar shara da ya yi tare da kama wani karamin ofis da kuma daukar ma'aikata har guda takwas don cimma burukan da ya sanya a gaba. Kuma tuni jama'a suka fara yabawa da wannan aiki nasu.

"Abu ne mai kyau ganin yadda suke yin aikinsu a nan, ga tsaftataccen muhalli wanda ya taimaka gaya wajan yadda suke aiwatar da ayyukansu".

"Mukan tara bola da yawa a nan wajan tun da wannan kanfanin na Global Services ya fara aiki gadan-gadan, muka fara samun banbanci kuma a bayyane".

Deutschlandlabor Folge 11 Übungsbild Müll
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Steffen

Kamfanin yana da motoci da suke daukar sharar a kullum zuwa wajen da ake sarrafasu a wajen birnin Lambarene inda bayan an tace sharar an dauki mai amfanin sai kuma a kona ragowar. Sai dai a cewar Makaya kona sharar na zama kalubale ga mazauna yankin.

"Wannan abu ne da ba shi da kyau, ba ma kawai yana shafar lafiyar masu aiki a wajen ba, har ma da shi kansa muhallin da muke kokarin karewa".

Yanzu abin da Makaya ya mayar da hankali shi da ma'aikatansa shi ne kokarin samar da na'urar da za ta dunga harhada robobi da sharar, kana da siminti don samar da bulo masu launin ja, wadanda za a dunga amfani da su wajen yin ayyukan gine-gine da kuma tituna, wanda tuni ma ya sayi filin yin aikin, sai dai matsala daya rashin isassun kudin da zasu mallaki ragowar kayan aiki.

"Tabbas jan aiki ne a gabanmu, kuma magana ta gaskiya duk da na san cewa akwai kalubale amma dai-dai da rana daya ban taba karaya ba, don na san nasara na tafe nan ba da dadewa ba.