1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Katsina an kafa kwamitin lura da bakin fiskoki

November 1, 2019

Sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta a jiharsa Mai martaba Sarkin Katsina Alh Abdul-muminu Kabir Usman ya kafa kwamiti wanda zai  duba yadda al'amuran jama'a ke gudana da kuma kula da baki.

https://p.dw.com/p/3SLjF
Nigeria Emirs-Palast Katsina
Hoto: DW

Wannan kwamiti dai ya kunshi hakimai sama da 40 na masarautar ta Katsina da jami'an tsaro da kungiyoyin sa kai. Mai martaba Sarkin ya ce irin rahotannin da yake samu kan gurbacewar al'amura a jihar yasa ya zama wajibi a matsayinsa na uba ya kara zage damtse dan kara bada gudummuwa da shawo kan al'amuran. 

Har ila yau Mai martaba sarkin na Katsina, ya bukaci 'yan kwamitin tsaro da aka nada da su yi aiki tsakaninasu da Allah dan tallafa ma talakawa wanda su abun ya fi shafa.

Nigeria Demonstration gegen Gewalt im Bundesstaat Katsina
Hoto: DW/Y. I. Jargaba

Alhaji Nuhu Abdulkadir Kauran Katsina, shi ne shugaban kwamitin da aka nada, ya kuma bayyanan wa DW cewa za su yi iyakar mai yiwuwa dan sauke nauyin da ya rataya wuyansu, bisa sharrudan da aka basu. 

A bangaren yadda masana harkar tsaro ke kallan wannan kwamiti da yinkurin sarakunan gargajiya wajen bada gudummuwarsu da magance matsalar tsaro a jihar Katsina, DW ta tuntubi Manjo Bishir Sha'aibu Galma mai murabus, Masanin tsaro a Nigeria, wanda ya ce dama can an bar batun tsaro ne daga tushe, domin harkar tsaro ba wai aiki ne na soja da dan sanda kawai, amma kowa na da gwadumawa da zai bayar, musamman sarakunan gargajiya, wadanda ke zama iyayen al'umma. 

Batun tsaro dai a jihar Katsina na cigaba da kwangaba kwanbaya, inda da an like can sai kuma can ya balle