1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin gyaran agogo a Bauchi da ke Najeriya

Aliyu Muhammad Waziri MNA
October 30, 2019

A jihar Bauchi wata matashiya ce ta rungumi sana'ar gyaran agogo domin yaki da zaman kashe. Yanzu haka tana samun alfanu na rufin asiri a cikin sana'ar.

https://p.dw.com/p/3SDxJ
Symbolbild Uhren Antiquariat
Hoto: Colourbox

Ko da yake matashiyar mai suna Khadija Sulaiman ta bayyana cewa ba haka kwatsam ta tsincin kanta cikin sana'ar ba, ta gada ne daga wajen mahaifinta wanda a yanzu ba ya iya fita domin gudanar da wannan sana'a.

A yanzu haka da wannan sana'a ta gyaran agogo wannan matashiya ke tallafa wa iyayenta har ma da biyan kudin karatunta da na kannenta. Khadija Sulaiman ta kara da cewa halin da ake a yau shi ya ba ta kwarin gwiwar kama sana'ar tare da ba ta muhimmanci kamar yadda ta yi karin haske.

Khadija Sulaiman ta bayyana cewa duk da mutane suna ganin kamar yanzu ba a samun wani abu a harkar gyaran agogo, ita kam gaskiya tana samu saboda kusan ita kadai ce a yankin take gyaran agogon wanda kusan babu ranar da za ta fito ba ta samu aiki ba. Ko akwai wasu nasarori da matashiyar ta samu.

Sai dai Khadija Sulaiman ta ce tana fuskantar kalubale daga wasu jama'a na rashin gamsuwa da kwarewarta a sana'ar saboda kasancewarta mace.