Salwantar rayuka lokacin neman tayar da bam a Sokoto
May 23, 2012A Jihar Sokoton Najeriya, wasu matasa fiye da 10 da ba a tantance ko su wane ba dauke da bindigogi sun kashe mutane biyu a safiyar wannan larabar ciki kuwa har da ɗan sanda, a kusa da Ofishin AIG na 'yan sanda dake kula da jihohin Sokoto kebbi da Zamfara. 'Yan bindigan sun kashe mutanen biyu ne bayan sallar asuba a lokacin da suka yi ƙoƙarin hana su ɗana wani Abu da ke fashewa,da ake kyauta zaton cewa Bomb ne.
Kwamishinan 'yan sandan Sokoto Sanda Aliyu ya bayyana cewar suna ci gaba da bincike don gano ko su waye ke da alhakin aikata aika-aikar. kawo yanzu dai babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin wannan yunƙuri na tayar da abu mai kama da bam. Sai dai Ahmed Aruwa da ke cikin waɗanda suka yi taho mu gama da 'yan bindigan ya bayyana takaicinsa game tabarbarewar tsaro a sokoto.
A daren jiya talata ma dai wasu 'yan fashi da makami suka yi wani fashi a wani Shagon sayar da magani Mai suna Zumunci a tsakkiyar Birnin sokoto, wanda ke zama irin sa na biyu a cikin kwannakki 3 da suka gabata.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas