Salman Khan ya soma zaman gidan yari
April 5, 2018Bayan zartas da hukuncin an tafi da Salman gidan yari don ya soma zaman wakafi bisa laifin kisan dabbar da ake kira gwanki ko Blackbuck. Tuni dai lawayansa ya shigar da kara don kalubalantar hukuncin, ana kuma ganin akwai yi yuwar a bayar da belin jarumin mai shekaru 52.
Wannan dai ba shi bane karon farko da jarumin ke baiyana a gaban kotu, don ko a baya an taba gurfanar da shi gaban kotu bisa laifin kade wasu mutane biyar da motarsa a shekarar 2002 lamarin da ya yi sanadiyar rayukansu, akwai kuma lokacin da aka same shi da laifin cin zarafin budurwarsa Ashwarya Rai wacce ita ma jaruma ce a fina-finan Bollywood na kasar.
Kotu ta yanke hukuncin a wannan Alhamis bayan kwashe shekaru ana gudanar da shari'a kan kisan dabbar da ya yi a shekarar 1998 ba tare da samun kwararran hujjoji da za su tabbatar da laifin kan Salman Khan ba sai a wannan lokacin.