SiyasaJamus
Saliyo za ta daina hukuncin kisa
July 24, 2021Talla
Akasarin 'yan majalisar da suka yi zama a kan batun a ranar Juma'a ne suka zabi yi wa hukuncin na kisa kwaskwarima a kasar ta Saliyo, abin da ya sanya za ta zama abin misali a nahiyar Afirka.
Maimakon yanke wa mai laifi hukuncin na kisa, yanzu an maye shi da daurin rai-da-rai ko kuma karanci zaman shekaru 30 a gidan yari.
Tun a shekara ta 1998 ba a sami wani da aka yanke wa hukuncin kisa ba a kasar ta Saliyo, duk da cewa ana aikata laifuka da suka kamaci hakan.
Tsarin mulkin kasar na shekarar 1991 ya amince da hukuncin kisa a kan 'yan fashi da wadanda suka aiakata kisa da cin amanar kasa da ma sojojin da suka yi wa shugabannisu bore.