1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saliyo ta janye kalaman sake bullar cutar Ebola

Yusuf BalaApril 7, 2015

A cewar jami'in lafiya daga cibiyar yaki da cutar ta kasa kuskure ne aka samu daga jami'an lafiya da suka dauki jinin da aka yi gwaji daga gawar mamacin suka ce yana da cutar.

https://p.dw.com/p/1F3sA
Symbolbild - Ebola
Hoto: Getty Images/J. Pollex

Mahukuntan a kasar Saliyo sun bayyana a wannan Talata cewa an tafka kuskure wajen bada rahoton cewa an sami rahoton wani dauke da cutar Ebola a Kailahu, wani yanki da ya zama dandalin wannan cuta a baya, da kuma bai samu wani da ke dauke da ita ba tsawon watanni hudu da suka gabata.

An dai bayyana cewa wani jariri dan watanni tara ya kamu da cutar ta Ebola wanda daga bisani cibiyar da ke lura da harkokin yaki da cutar ta Ebola ta kasa ta gano cewa yaran ya rasu ne ta sanadin wasu cutikan ba cutar Ebola ba kamar yadda Sidi YahayaTunis mai magana da yawun cibiyar ya bayyana.

Ya ce kuskure ne aka samu daga jami'an lafiya da suka dauki jinin da aka yi gwaji daga gawar mamacin.

Kimanin mutane 3,800 ne suka rasu ta sanadin cutar ta Ebola a kasar ta Saliyo sai dai wannan adadi na ci gaba da yin kasa a sakamakon himma da ma'aikatan jiyya ke sawa a yaki da wannan annoba.