1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antonio Guterres zai ziyarci Libiya

Yusuf Bala Nayaya
April 3, 2019

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa zai ziyarci Libiya don kaucewa samun sa-in-sa tsakanin bangarori biyu da ke gaba da juna a kasar.

https://p.dw.com/p/3GBtc
Den Haag Schlusszeremonie des UN-Kriegsverbrechertribunals für Ex-Jugoslawien | UN-GeneralSekretär Antonio Guterres
Hoto: Reuters/United Photos/T. Kluiters

Antonio Guterres ya bayyana haka ne a wannan Laraba a lokacin da suke tattaunawa da Shugaba Abdel-Fattah el-Sissi na Masar a yayin da yake kammala ziyararsa ta kwanaki biyu a birnin Alkahira. Guterres ya ce yana fatan ganawar da aka yi a farkon shekara a Abu Dhabi tsakanin Khalifa Haftar jagoran sojojin na Libiya da Fayez Sarraj shugaban gwamnatin ta Libiya da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya, za ta zama muhimmin mataki na hade kan bangarorin da ba sa ga maciji a Libiyar.

Ziyarar ta Guterres zuwa Libiya na zuwa makonni biyu kafin taron kasa da aka shirya bisa shiga tsakanin MDD, a kokari na shata hanyoyi da za a dora Libiya don warware rikicin da ta fada tun bayan hambarar da Moammar Gadhafi a 2011.