Sakamakon zaben shugaban kasar Gabon
November 30, 2005A kasar Gabon hukumar zabe mai zaman kanta, ta bada sakamakon zaben shugaban kasa da a ka yi ranar lahadi da ta wuce.
Shugaba Omar Bango da ke kan karagar mulkin kasar tun shekara ta 1967, ya yi tazarce, tare da kashi kussan 80 bisa 100, na illahirio kuri´un da a ka jefa.
Dan takarar jamiyar adawa Piere mambundu ya zo sahu na 2 tare da kimaninkashi 14 bisa 100.
Gabanin bayana sakamakon Mambundu yayi shelar cewa shi ya lashe zaben.
Ko kamin bada sakamakon, manazarta al´ammura a kasar, sun tabbatar da cewa, Omar Bango samu gagaramar nasara.
Yan kallo daga kungiyar kasashe masu anfani da halshen Fransanci ,da kuma na kungiyar kasashen yankin tsakiyar Afrika, da na Amerika da Fransa, sun yi tabaraki ga zaben ,da su ka shaidi cewa ,ya gudana cikin kwanciyar hankali da adalci.
A nasu gefe yan takara 2, da su ka zo na 2, da na 3, sun kiri taron manema labarai, inda su ka yi watsi da sakamakon zaben, tare da zargin tabka magudi da aringizon kuri´ u.