Sakamakon zaɓen ƙasar Zambiya
September 23, 2011Hukumar zaɓe a ƙasar Zambiya ta baiyana jagoran 'yan adawa Michael Chilufiya Sata a masayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a bisa abokin takararsa shugaba mai barin gado Rupiah Banda. Hukumar zaɓen ta ce mista Sata ɗan shekaru kimanin 70 da haifuwa ya samu kashi 43 cikin ɗari na ƙuriun da aka kaɗa yayin da abokin hamaiyar sa Rupiah Banda ya samu kashi 36 cikin ɗari na ƙuri'un.
Tun da farko dai jinkirin da aka samu wajen baiyana sakamakon zaɓen wanda aka gudanar tun ranar talatar da ta gabata ya janyo fushin 'yan adawar da suka fantsama akan tituna don gudanar da zanga zanga wacce mutane biyu suka rasa rayukansu a wasu garuruwan guda biyu da ke a yankin tsakiyar maso arewacin ƙasar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala