Safarar mata domin karuwanci Ghana
August 20, 2019Tessy wadda ba sunan ta na gaskiya kenan ba, ta ce a kullum mata daga sassan kasashen Afirka ke sintiri a titin Nagasaki a birnin Tamale, burinsu shi ne su sami namiji da zai kwana da su ya biyasu kudi, ba wai matan sun tsara wa kansu haka bane, sun sami kansu ne cikin wannan yanayi bayan da suka nemi gujewa talauci a kasashensu na asali don neman aikin inganta rayuwa. A yayin neman mafita suke fadawa tarkon masu safarrar mutane da ke ci da gumin su.
''Matar da ta kawo ni, ta ce da ni zan yi mata aiki ne a shagon sayar da tufafi, sai bayan da na zo ta ce, karuwanci zan yi, bani da zabi, dole na yarda, don ko na fadawa 'yan sanda, kama ni kawai za su yi, su tsare ni''
Sai dai kuma wata wadda ta bukaci a sakaya sunanta cewa ta yi ba ta zubar da mutuncinta wajen neman kudi ba, gara ta koma gida Najeriya, domin ko lokacin da ta ke gida bata karuwanci, iyayen ta na da karfin biya mata bukatunta''