1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar Takaddama tsakanin sojojin Nijar da kungiyar EU

Gazali Abdou Tasawa
November 25, 2024

Al'ummar Nijar suna tofa albarkacin bakinsu kan sabon takun sakar da aka shiga tsakanin gwamnatin mulkin sojan kasar da kungiyar Tarayyar turai EU kan kudaden tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta yi wa barna

https://p.dw.com/p/4nPt6
Archivbild I Bamako, Mali -Unterstützer feiern nach Militärputsch
Hoto: AP/picture alliance

Wannan sabon takun saka ya taso ne bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nijar  ta nuna rashin amincewarta dangane da yadda kungiyar Tarayyar Turai ta yi gaban kanta wajen kashe kudade Euro miliyan daya da dubu 300 da EU din ta ware da sunan taimaka wa mutanen da ambaliyar ruwa ta yi wa barna a daminar bana a kasar ta Nijar.

A kan haka ne gwamnatin Nijar ta bukaci kungiyar ta EU da ta gudanar da bincike kan yadda kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na kasa da kasa da ta bai wa wadannan kudade domin gudanar da ayyukan jin kai suka kashe kudin a Zahiri.

Lamarin dai bisa ga dukkan alamu ya harzuka kungiyar EU wacce ta dauki matakin kiran jakadanta a Nijar koma wa Brussels domin bayar da bahasi. Ko da shike ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta bayyana cewa ita ce da kanta ta bukaci kungiyar ta EU da ta janye jakadan nata.

Da yake tsokaci, Malam Oumarou Kane wani dan jarida mai sharhi kan harkokin yau da kullum ya ce kungiyar EU ba ta da gaskiya a cikin wannan rikici.

To sai dai wasu ‘yan Nijar din na ganin kungiyar Tarayyar Turan na da gaskiya wajen kin mika wa gwamnatin irin wadannan kuade na kawo tallafi ga talakawa . Malam Siraji Issa na kungiyar MOJEN na daga cikin masu irin wanann ra’ayi.

Sai dai kungiyar MOJEDEC ta bakin shugabanta Malam Abou Reid Sanoussi Abdoulaziz ta ce akwai bukatar kai zuciya nesa tsakanin bangarorin biyu a cikin wannan sabani domin kauce wa saka talakawa cikin garari.

Abin jira a gani a nan gaba shi ne yadda za ta kaya tsakanin gwamnatin mulkin sojan ta Nijar da kuma kungiyar ta EU a cikin wanann sabon takun saka.