Sabuwar hanyar yaki da cin hanci a Najeriya
February 13, 2017Tsarin na yaba kyauta tukuici da gwamnatin Najeriyar ta bullo da shi a yaki da take da masu halin bera da ta ce sun wawashe asusun gwamnati a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya kama mulki ya fara nuna samun nasara saboda makudan kudin da gwamnatin tace ya zuwa yanzu ta samu nasarar kwatowa ta dalilin bayanai na tonon asiri da gwamnatin ta samu ta hannun ‘yan Najeriya.
Fara amfani da wannan tsari ya sanya gwamnatin Najeriyar samun nasarar karbo Dala miliyan 15 da kuma Naira biliyan takwas daga mutanen da ake zargin sun wawashe dukiyar kasa. Shin me wannan ke nunawa ne ga wannan sabuwar doka da ke taimaka bankado kudadden da aka sace aka jibgesu a gidaje a kasar? Barrister Mainasara Umar kwararre a fannin dokokin Najeriya na mai bayyana abin da wannan ke nunawa.
Samun sauyi daga daukacin lamarin yaki da cin hanci da rashawa da a lokutan baya ‘yan Najeriya kan nuna halin na zaman ‘yan marina, na ba ruwan kowa daga abinda ke faruwa. Mr Lai Mohammed ministan yada labaru na Najeriya na mai bayyana abin da suka hango ga tasirin wannan.
Ya ce "Wannan tsari na tona asirin wadanda suka saci dukiyar gwamnati na biyan bukata domin mun samu bayanai da suka sanya kwato Naira milyan 131 a rana guda baya ga wasu kudadden da aka samu, ga kuma kudadden da aka gano a gidan tsohon shugaban hukumar mai ta NNPC, don haka muna murna da ganin tasirin tsarin.''
An cikin wannan ne dai hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta EFCC ta samu kwato sama da dalla milyan 9 da pam dubu 74 daga gidan tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC da ake zargin da aikata ba dai dai ba. Abin da ya sanya Barrsiter Mainasara bayyana cewa hukunta irin wadannan laifuffuka na bukatar sake lale.
A yayin da gwamnatin ke murna ta samun kwato dukiyar kasa daga wadanda take zargi da nuna halin bera, ga al'ummar kasar na zura idanun ganin gwamnati ta yi amfani da kudadden da take kwatowa domin ci gaban kasa, musamman fanin rage radadin talauci da shi ne ya fi adabar ‘yan Najeriya a yanzu.