1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Badakala a majalisar dattawa ta Najeriya

March 13, 2024

A yayin da miliyoyin mutane a cikin Najeriya ke dada nisa a karatu na sadaukarwa domin ginin kasa, ana kara ganin alamun cin hanci a majalisar dattawa ta kasar bisa kasafin kudin kasar na shekarar bana.

https://p.dw.com/p/4dTYw
Majalisar dattawa ta Najeriya lokacin gabatar da kasafin kudi
Majalisar dattawa ta Najeriya lokacin gabatar da kasafin kudiHoto: Ubale Musa/DW

Wani zargin ware wasu kudi Naira tiriliyan sama da uku ne dai ke neman tono dagwalon da ke majalisar a halin yanzu. Kuma duk da cewa dai majalisar tai nasarar dakatar Sanata Abdul Ahmed Ningi da ke zaman allura ta bankado almundahanar, daga duk alamu majalisar tana da jerin tambayoyin amsawa cikin rikicin kudin da ke majaliyar yanzu.

Karin Bayani: Kira kan kyautata mulki a Afirka

Kudin Najeriya na Naira
Kudin Najeriya na NairaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Akalla Naira miliyan dari biyar ne dai aka sanya a cikin kasafin kudin kasar na shekarar bana domin amfanin kowane guda cikin wasu jiga-jigan 'yan majalisar 34. Shi kansa uban tafiyar kuma shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio dai ya kai gida da Naira miliyan dubu biyu da rabi domin sayen janareton ba da wuta da firjin sanyi a mazabarsa. A wani abin da ke neman tabbatar da zargin farko sannan kuma ma'aunin irin dattin da ke a zauren yin doka na kan gaba a Najeriya.

Ya zuwa yanzun dai masu mulkin kasar sun yi nisa cikin karatun rokon miliyoyin 'yan kasar da ke ji a jiki sakamakon manufofin gwamnatin kasar na kare tallafi ga rayuwa ga makoma. Kuma tun ba#a kai ga ko'ina ba dai ana Shirin raba gari a tsaklanin yan mulki da kungiyoyin kallo da ke fadin an saba a cikin tsarin dimokaradiyya a kasar.