1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin warware rikicin Boko Haram

May 28, 2014

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce, ya fara tattaunawa da wasu na kusa da 'ya'yan Kungiyar Boko Haram, da ke garkuwa da 'yan matan Chibok.

https://p.dw.com/p/1C8TS
Olusegun Obasanjo
Hoto: Braima Darame

Ta dai kai ga dagun kara ta kuma ce a kai ga kasuwa, to sai dai kuma tana shirin fuskantar kari na matsin lamba ga gwamnatin Tarrayar Najeriya da ta ce ba ta da niyyar sulhu da masu sana'a ta ta'adda amma kuma ke shirin ganin sulhu a bakin kofar ta.

Na baya-baya cikin yunkurin sulhun dai na zaman tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo da ya fara nuna alamar taka rawa da kuma tuni ya kai ga ganawa da wasu da ke kusa da jami'ai na kungiyar, Obasanjon da yanzu haka ke can birnin London dai ya ce, ya kai ga bude ganawa da na kusa da 'yan kungiyar da ke cigaba da rike yaran har na tsawon makwanni kusan bakwai.

Sabon matakin da ke zuwa dai-dai lokacin da gwamnatin kasar ke musanta rushewar wani irinsa da wani dan jarida mai zaman kansa ya jagoranta dai, a cewar Senata Ali Ndume da ke zaman dan majalisar dattawan da ke wakiltar 'yan matan na Chibok na zaman abun farin ciki ga daukacin iyayen yanki:".

Frankreich Paris Boko Haram Gipfel 17.5.2014
Goodluck da HollandeHoto: Alain Jocard/AFP/Getty Images

"Obasanjo ba karamin mutun bane kamar yadda na fada kuma in ma akwai kura-kurai na gwamnati shi ba bako bane, ya kamata a zauna a sirrance a tattauna. Babban abu shi ne, duk duniya ana kukan yadda za'a ceto 'yan matan nan kuma duk abun da za'a yi a samu a ceto su ya kamata a goya masa".

Kishin kasa da kokari na ceto yara ko kuma siyasa da makomar 'yan matan na Chibok dai shekaru ukun da suka gabata dai yunkuri na tsohon shugaban ya kai ga ziyartar birnin Maiduguri da nufin lallashi ga yan kungiyar da a wancan lokaci suka kai ga ta'azzarar hare hare kan al'ummar yankin.

Ziyarar kuma da ta kare da kisan babban mai masaukinsa kuma suruki ga tsohon madugun kungiyar Mohammed Yusuf a birnin Maiduguri. A wani abun da aka rika kallo alamu na rashin amincewa da shugaban a bangaren 'ya'yan kungiyar. Abun kuma da ke iya kaiwa ga kara jefa rayuwar yaran cikin sabuwar barazana ta makoma.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar