Sabon musayar wuta a Ukraine
September 17, 2014Talla
Dama dai a 'yan kwanakin an saba jin karar harbe-harbe tsakanin bangaren gwamnatin Kiev da na 'yan awaren a yankin da ke da masana'antu wanda kuma 'yan aware masu goyon bayan Rasha ke da karfi duk kuwa da sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka yi. 'Yan awaren masu goyon bayan Rasha dai sun yi maraba da batun tagaita wutar sai dai sun kafe a kan cewa dole ne a basu 'yancin cin gashin kansu a matsayin kasa mai cikakken iko da suka kira da "New Rasha" wato sabuwar Rasha ke nan. Kasashen Yamma dai na zargin Rasha da iza wutar rikicin Ukraine din da aka kwashe tsahon watanni biyar ana yi, zargin da mahukuntan Moscow ke ci gaba da musantawa suna masu cewa ba hannunsu a ciki.