Sabon matakin yakar Ebola
September 29, 2014Shirin Majalisar Dinkin Duniya na yaki da bala'in annobar cutar Ebola wato 'UNMEER' zai bude helkwatarsa a kasar Ghana domin rarraba kayan agaji a yankin yammacin Afirka da cutar ta addaba. Ana sa ran shugaban shirin Anthony Banbury da tawagarsa za su isa Accra babban birnin kasar ta Ghana domin tattauna yadda ayyukansu zasu kasance. Shirin na 'UNMEER' zai duba babban abin da aka fi bukata domin yakar cutar musamman a kasashe uku da ta yi wa katutu wato Laberiya da Gini da kuma Saliyo.
Daga nan kuma za su tabbatar da ganin cewa magunguna da jami'an kiwon lafiya sun isa ga yankunan da ke da tsananin bukatar agaji. Cutar ta Ebola dai kawo yanzu ta hallaka sama da mutane 3,000 a ksashe hudu na yankin yammacin Afirkan da ta bulla.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita. Suleiman Babayo