SiyasaTarayyar Rasha
Rasha: Sauye-sauye a ma'aikatar tsaro
May 20, 2024Talla
A makon da ya gabata Shugaba Vladimir Putin na Rashan ya dauki wani mataki da ya bayar da mamaki, inda ya sauke tsohon ministan tsaro Sergei Shoigu tare da maye gurbinsa da Andrei Belousov da ke zaman kwararre a fannin tattalin arziki kana tsohon ministan lura da tattalin arzikin Rashan. Wannan matakin dai na nuni da yadda Putin ke kawo gagarumin sauyi a ma'aikatan tsaron Moscow, wadda ke fama da rikici da ke da nasaba da cin-hanci da rashawa.