Jamus ta kaddamar da sabbin manufofi kan China
July 13, 2023Gwamnatin Jamus ta bayyana sabbin manufofin cinikayya da kasar China, bayan tattaunawa tsakanin jam'iyyun da ke cikin gwamnatin kawancen ta Jamus, inda aka amince da rage kasadar da ke cikin cinikyayya da China, wadda take zama babbar abokiyar cinikayyan Jamus.
Annalena Baerbock ministare harkokin wajen kasar ta Jamus ta bayyana manufofin a cibiyar kula da harkokin China da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Sannan Baerbock ta kara da cewa Jamus tana bukatar aiki da China, amma China kuma tana bukatar kasashen Turai. Yanzu Jamus ta dauki matakin karfafa zuba jari a wasu kasashen duniya masu samun tagomashin tattalin arziki.
Sabbin maniufofin za su taimaka wa Jamus wajen rage dogaro da China, tare da samun kayayyakin masana'antu daga wasu bangarorin na duniya.