Sabbin hare-hare a Maiduguri
March 7, 2015Bam na farko ya tashi ne da misalin karfe 11:25 na safiyar yau a babbar mashigar kasuwar kifi da ke tashar Baga inda ake zargin wata mata ‘yar kunar bakin wake ta tada shi kuma kusan mutane 20 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikata. Bam na biyu kuma ya tashi ne da misalin karfe 12:05 na rana a babbar kasuwar Maidugiri da ake kira Monday market kusa da Post Office.
Daga bisani kuma rahotanni daga kamfanin dillancin labaran Associated Press, sun tabbatar da cewa an kara jin fashewar wani abu a karo na uku duk a cikin kwaryar Maiduguri. Sai dai babu cikakken bayani na yawan wadan da abin ya rutsa da su a tashin bam na biyun da kuma na ukun ya zuwa yanzu. Ga dai abunda wani shaidan gani da ido a tashin bam na farko a tashar Baga ke shaidawa wakilin DW ta wayar tarho bisa sharadin ba za a bayyana sunan sa ba.
"Yanzu haka ‘yan kasuwa sun rufe shagunan su a wadannan wuraren inda masu aikin ceto ke ci gaba da jigila tare da kulawa da wadanda hare-haren suka rutsa da su, haka nan kawo yanzu babu wani ko wata kungiya da ya dauki alhakin kai harin, ko da yake kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar ta saba kai makamantan wadannan hare-hare."
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba