1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan sama ya hallaka mutane a Indiya

Abdourahamane Hassane
May 3, 2018

Mutane 100 suka mutu kana wasu 140 suka jikkata a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka a arewacin Indiya daga daran Larba zuwa Alhamis (03-05-18).

https://p.dw.com/p/2x7TF
Indien Sturmschaden in Alwar
Hoto: Reuters

Hukumomin Indiyan sun ce Jihohin Uttar Pradesh da Rajasthan su suka fi shafuwa inda aka samu asarar rayuka sossai, sannan sun ce addadin wadanda suka mutun zai iya karuwa a cikin awowi na gaba masu zuwa. Yawancin wadanda suka mutun gine-gine ne suka ruguza da su.