Rundunar sojin Nijar ta kashe jigo a kungiyar IS
June 23, 2024Talla
Rundunar sojin Nijar ta ce ta samu nasarar kashe babban jigo a kungiyar ta IS, Abdoulaye Souleymane Idouwal tare da wasu 'yan ta'adda tara ne a yayin musayar wuta a yankin Tillaberi da ke kusa da iyakar kasar da kasashen Mali da kuma Burkina Faso. Rundunar ta kuma kara da cewa, ta kama wasu 'yan ta'addda 31 a lokacin, ta kuma lalata duk wata hanyar sufuri da kuma sadarwarsu.
Karin bayani:Sojojin Nijar sun halaka 'yan ta'adda a Tillabery
Yankin Tilaberi dai ya sha fama da matsalar 'yan ta'adda inda gwamantin mulkin sojin kasar ke ci gaba da yakar mayakan Boko Haram da ISWAP a wasu sassan kasar.