1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a babban taron jam'iyyar Republican

Kabir Isa Jikamshi/ASJuly 19, 2016

Babbar jam'iyyar adawa a Amirka wato Republican ta fara babban taronta gabannin zaben shugaban kasa da za a yi nan da 'yan watannin da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1JRw3
USA Cleveland Parteitag der Republikaner Donald Trump
Hoto: Reuters/C. Allegri

Taron wanda ake gudanarwa a birnin Cleaveland na kasar ta Amirka dai ya nuna irin zargin da ake yi na rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar gabannin tabbatar da Donald Trump a matsayin mutumin da zai yi wa jam'iyyar takara a zaben shugaban kasa. A shi wannan taro dai, da dama daga cikin 'yan jam'iyyar sun bukaci da a sauya wasu dokokin jam'iyyar wanda za su taimaka wajen hana Trump yin takara.

Wani abu har wa yau da taron ya fuskanta wanda a baya ba ga irinsa ba shi ne yadda wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar suka kauracewa babban taron. Wadannan mutane dai sun hada tsohon shugaban kasar George Bush da Sanata John McCain da kuma Mitt Romney. To sai dai duk da wannan, an gudanar da jawabai a shi wannan taro kuma sun fi maida hankali ne kan batun tsaro a Amirka.

USA Melania Trump in Cleveland
An zargi Melania Trump da satar wani bangare na jawabin da Michelle Obama ta yi a 2008Hoto: Getty Images/A. Wong

To baya ga wannan batu, wani abu har wa yau da ya ja hankalin mutane shi ne jawabin da mai dakin Trump wato Melania Trump ta yi. Wani bangare na jawabin nata dai ya yi kama da irin jawabin da matar Shugaban Obama wato Michelle Obama ta yi a 2008 lokacin da ya ke neman shugaban kasar karkashin jam'iyyarsa ta Demokrat. Da dama dai sun yi ta tsokaci da kuma Allah wadai dangane da wannan abu, inda wasu ke ganin hakan zai iya sanya rashin yadda da ma dawowa daga rakiyar tafiyar ta Trump sai dai jami'an yakin neman zaben na Trump na cewar jawaban mutane biyun sun yi kamanni ne sakamakon irnin tunani guda da suke da su kan batutuwa da dama.