1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Niger Delta a Najeriya

May 22, 2009

Jaridun sun fi mayar da hankali kan rikicin Nger Delta da ƙasar Somaliya inda sojojin sa kan Islama ke ƙara samun galaba.

https://p.dw.com/p/HvR6
Tsagerun Niger DeltaHoto: AP

A wani rahoto mai taken tashe tashen hankula a yankin Niger Delta jaridar Neues Deutschland ta fara labarin ne da cewa fararen hula a tsakiyar fagen daga tana mai nuni da mummunar musayar wuta tsakanin ´yan tsagerun wannan yanki da kuma dakarun gwamnati, wanda haka ya sa ƙungiyar MEND ta ƙaddamar da abin da kira yaƙi gadangadan kan gwamnatin tarayya. Ta ce mazauna wannan yanki mai arzikin man fetir sun shafe sama da shekaru 50 suna cikin halin ƙaƙanikayi inda suke ƙorafin cewa duk da tatsar arzikinsu da ake yi har yau su ba su gani a ƙasa ba. Jaridar ta ƙara da cewa yankin ya sake faɗawa cikin wani rikici sakamakon farmakin da sojojin Nijeriya ta yi iƙirarin kaiwa a kan ´yan tawayen to amma mazauna yankin sun ce a kan fararen hula ake lugudan wutar. To sai dai kakakin rundunar sojin Nijeriya ya musanta wannan zargi. Jaridar ta rawaito Victor Burubo kakakin ƙungiyar al´umar Ijaw na kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta tsoma baki.

Somalia Soldat aus Äthopien in Somalia
Sojin Ethiopia a SomaliyaHoto: AP

Har yanzu babu tabbas ko dakarun Ethiopia sun sake kutsawa cikin Somaliya ko kuma kan iyakokinsu suke karewa don hana yaƙin basasan Somaliya bazuwa cikin ƙasarsu, inji jaridar Berliner Zeitung a sharhin da ta rubuta game da ɓarkewar tarzoma a Somaliya. Ta ce da yake har yanzu an kasa haɗa kan dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da za a tura Somalia, wataƙila wasu membobin Kwamitin Sulhu za su yi murna idan dakarun Ethiopia suka kutsa Somalia don ceto gwamnatin riƙon ƙwarya daga matsin lambar sojojin sa kai na Islama. To sai dai yaƙin basasa da mawuyacin hali da ´yan gudun hijira ke ciki a yankin ƙahon Afirka ba ya da wani muhimmanci ga kafofin yaɗa labaru na yankin. Da farko ´yan fashin jiragen ruwa a Somaliya, ƙasar dake zama misali na jerin ƙasashe da suka wargaje, sun maido da ita a kanun labaru, tun sannan ake muhawara kan yadda za´a yaƙi ´yan fashin na cikin teku. Jaridar ta ce har yanzu lalabe ake cikin duhu.

Milizen im Darfur
´Yan tawayen DarfurHoto: picture-alliance/ dpa

Dakarun Ethiopia a Somalia taken rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung kenan inda ta rawaito waɗanda suka shaida abin da ya faru suna cewa sojojin Ethiopia ɗauke da makamai sun toshe hanyoyin mota a kewayen garin Beledweyne dake kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

A karon farko wani da ake zargi da aikata laifukan yaƙi a Darfur ya miƙa kansa ga kotun ƙasa da ƙasa dake shari´ar masu aikata manyan laifuka. A rahotonta jaridar Die Tageszeitung ta ce Bahr Idriss Abu Garda madugun ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ´yan tawayen yankin Darfur ya musanta zargin da ake masa ciki har da kai hari kan dakarun kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka a yankin Haskanita inda aka kashe sojojin AU 12 sannan takwas suka samu raunuka. To sai dai wannan harin ba komai ba ne idan aka kwatanta da cin zarafin da aka aikata kan bil adama wanda yayi sanadiyar mutuwar dubun dubatan mutane wanda kotun ta birnin The Hague ta ɗora laifin kan gwamnatin Sudan.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed