Rikicin tawaye na neman sake barkewa a Chadi
March 22, 2013Talla
Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewar kungiyoyin sun yi wata ganawarsu ce a birnin Doha na kasar Qatar da nufin cimma matsaya guda domin kifar da shugaba Deby daga kan karagar mulkin kasar.
A shekara ta 2008 ne shugaban kasarya ketare rijiya da baya a lokacin da sojojin faransa suka taimaka masa korar 'yan tawayen daga fadarsa, to saidai a wannan karon gwamnatin Francois Hollande ta ce ko kusa baza ta saka hannunta ba a cikin rikicin cikin gidan Chadin ko da ya barke..Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar ya aika da kimanin dakarun kasar dubu biyu a kasar Mali domin yakar kungiyoyin kishin addini.
Mawallafi: Issouhou Mahamane
Edita: Halima Balaraba Abbas