AU za ta yi taro kan tsaro
February 9, 2020Talla
Jigon taron na kwanaki biyu shi ne jaddada fatan kungiyar Tarayyar Afirka AU na kawar da yaduwar bindigogi da makamai a nahiyar Afirka nan da shekarar 2063, matakin da kungiyar ta dasa damba a 2013 da zimmar farfado da ingantaccen tsaro a kasashen Afirka.
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai halarci taron don neman mafita kan rikicin Libiya. Ana kuma kyautata zaton taron zai karkare da cimma sauya shugabancin AU daga Masar zuwa Afirka ta Kudu.