Lamura na kara sukurkucewa a Libiya
January 4, 2020Janar Khalifa Haftar habsan soja mai karfi da ke rike da gabashin kasar Libiya ya soki matakin gwamnatin Turkiyya na shiga rikicin da ke faruwa a kasar ta Libiya, inda ya bukaci mutane su dauki makamai domin kare kasar. Ita dai Turkiyya ta shiga rikicin domin taimakon gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya mai mazauni a birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar.
Akwai wasu kasashen Laraba da ke goyon bayan Janar Khalifa Haftar abin da masana ke ganin shiga rikicin da Turkiyya ta yi ka iya dagula a lamura a kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka, wadda ta fada rikici tun shekara ta 2011 bayan faruwar gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.
An soke tashi da saukan jiragen sama a filin jiragen sama na birnin Tripoli sakamakon fada da ya barke tun ranar Jumma'a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna aksar ta Libiya.