Takaddama tsakanin Amirka da Chaina ya janyo martani
May 10, 2019An dai kai ga wannan matakin ne bayan da bangarorin biyu suka gagara cimma matsaya a zaman da suka yi da wakilan Chaina da Amirka a makon jiya, Chaina ce ta fara sauya daftarin yarjejeniyar da suka kulla kan batun kasuwancin a baya, wanda ga duk alamu bai yi wa Amirkan dadi ba, inda Shugaba Donald Trump ya sanar da sanya doka kan yin karin kudin harajin ga duk hajjojin Chaina da ke shiga kasarsa. Dokar da ta soma aiki daga wannan Jumma'a, sai dai acewar mataimakin Firaiministan Chainan Liu He da ya wakilci zaman yana cike da fata za su iya shawo kan matsalar.
Yana ganin huldar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu za ta dore duk kuwa da barazanar da Chaina ta yi na mayar da martani. Tuni dai sauran kasashe kamar Faransa suka nuna fargaba, Faransa dai ta ce akwai damuwa kan barazanar da tattalin arzikin duniya ka fuskanta bisa wannan rikicin da ya kunno kai kamar yadda Ministan kudi na Faransa Bruno le Maire ya fadi a tattaunawar da aka yi da shi ta kafar talabijin a kasar,
Dama dai, mataimakin Firaiministan Chaina ya ce akwai bukatar yi wa batun taron dangi don samun mafitar da ita ce a bi hanyar laluma don yi wa tufkar hanci.
Matakin na Amirka na lafta wa kayayyakin Chaina karin haraji daga kashi 10 zuwa kashi 25 cikin 100 kan duk hajjoji na Chaina da za su shiga kasar, zai kasance batu da masana za su ci gaba da yin sharhi kai na tsawon lokaci, kafin nan an zura ido don ganin abin da zai biyo baya.