Rikicin Libiya na kara lakume rayuka
April 12, 2019Talla
Akalla mutane 56 ne aka kashe cikin kwanaki shida na fadan da ya barke a kusa da babban birnin kasar Libiya kamar yadda Hukumar Lafiya ta MDD (WHO) ta bayyana, inda ta yi gargadin cewa muddin fadan bai tsaya ba za a ci gaba da rasa rayuka. Har ila yau Hukumar WHO ta ce akwai kuma wasu mutane 266 wadanda suka samu raunuka.
Ita ma dai Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kamar yadda Steffen Seibert ya bayyana ta bi sahu na Kungiyar Tarayyar Turai inda a ranar Alhamis ta yi kira ga Khalifa Haftar da ke jagorantar sojoji masu kai farmaki ga bangaren gwamnati da MDD ta amince da ita ya dakatar da fadan ba tare da bata lokaci ba.
Tun bayan da fadan ya barke a kudancin birnin Tripoli dubban al'umma da ke yankin ke kaurace wa muhallansu.