1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin jam'iyyar Labour ya dauki wani salo a Najeriya

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
October 10, 2024

Rikicin jam'iyyar adawa ta Labour a Najeriya ya sake daukar sabon salo bayan da babbar kotu ta tialsta wa hukumar zabe amincewa da shugaban jam'iyyar, Julius Abure a matsayin halastaccen shugaba.

https://p.dw.com/p/4ldFJ
Dan takarar Labour a zaben Najeriya na 2023, Peter Obi
Dan takarar Labour a zaben Najeriya na 2023, Peter Obi Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Bayyana Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour a Najeriya, ya faru ne duk da adawar da banagren dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peter Obi ke yi da hakan.

Wannan mataki da aka dauka a yanzu ya katse hanzarin masu adawa da shugabancin nasa da ya sanya turnikewar rikici har da doke-doke a hedikwatar jamiyyar a tsakanin bangarorin biyu.

A yanzu dai kotu ta raba gardama a kan wannan rikici na cikin gida abinda ya sanya murna ga bangaren Julius Abure.

Sai dai da alamun cewa akwai sauran rina a kaba a kan wannan batu domin wadanda suka ja daga a kan wannan rikici na jam'iyyar ta Labour musamman ganin yadda gwamnan jihar Abia Alex Otti da dan takarar neman shugaban kasa na jamiyyar ta Labour Peter Obi suka kai ga nada Misis Nenadi Usman a matsayin shugabar kwamitin riko, don nuna rashin amincewarsu da babban zaben jam'iyyar da ya samar da shugaban jamiyyar na yanzu.

Shugbancin jam'iyyar siyasa a Najeriya shi ne mafi santsi a tsarin dimukuradiyya a kasar. Kama daga jam'iyya mai mulki zuwa ga ta 'yan adawa, manya da kanana duka kanwar ja ce; ta rikicin da ke awon gaba da shugaban jamiyya.

Har yanzu dai tsugune ba ta kare ba a jam'iyyar ta Labour, yayin da hukumar zaben da aka tilasta wa amicewa da shugabancin Abure ke jiran abin da zai biyo bayan daukaka karar da aka yi.