1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sasanta kasashen biyu na tsakiyar Afirka

June 30, 2020

Kassashen Kamaru da Equatorial Guinea sun janye dakarunsu daga iyakokin kasashen guda biyu, biyo bayan 'yar hatsaniya da ta shiga tsakanin dakarun da ta yi sanadiyar hallaka mutane bakwai.

https://p.dw.com/p/3eapl
Grenze zwischen Äquatorialguinea und Kamerun
Hoto: DW/E. Asen

Rikicin iyaka tsakanin Kamaru da Equatorial Guinea abu ne da ya jima yana daukar hankullan mahukuntan kasashen biyu tare da takurawa mazauna garuruwan da ke dab da iyakokin, wani al'amari na baya-bayan nan da ya rura wutar rikicin shi ne wani bango da Equatorial Guinea ta fara ginawa domin killace kanta tare da hana 'yan Kamaru shiga yankunanta. Masu fada a ji a kasashen guda biyu da suka hada da masu rike da masarautun gargajiya da jami'an gwamnatin kasashen ne suka zauna domin lalubo bakin zaren warware matsalar. Leandro Bekale Nkogo wanda shi ne ministan harkokin tsaron Guinea ya ce sun dauki wannan matakin ne domin fuskantar abokan gaba ta yadda za a gudu tare a tsira tare: '' Abin da muke bukata shi ne a samu cikakken hadin kai tsakanin sojojin Kamaru da na Guinea domin fuskantar 'yan ta'adda a yankin kogin Guinea da kuma masu dauke da makamai da ke zafafa kai hare-hren ta'addancin kan farar hula da ba su ji ba su gani ba.''

Dukkanin kasashen biyu sun amince da shirin samar da zaman lafiya

Grenze zwischen Äquatorialguinea und Kamerun
Hoto: DW/E. Asen

A yayin taron, shi ma ministan tsaron Kamaru Joseph Beti Assomo ya bukaci kasashen guda biyu da su cigaba da zama abokan juna duba da dadaddiyar alakar da ke tsakaninsu. Rikicin dai na baya-bayan nan da ya kunno kai ya tilasta wa 'yan kasuwa da manoman da ke zaune a iyakokin kasashen barin muhallansu domin su tsira da rayyukansu, Angela Amende wata 'yar kasuwa ce kuma 'yar asalin kasar Kamaru da ke safarar barasa daga Equatorial Guinea cewa ta yi ba ta yi tsammanin rikicin iyaka tsakanin kasashen biyu ya yi tsanani kamar haka: '' Kullum shugabannin kasashen Kamaru da Guinea da zarar suka bude baki sai su ce sun lashi takobin sasanta rikicin iyakar da ke tsakaninsu, amma har yanzu shiru ka ke ji sai ma abin da ya yi gaba, kamata ya yi shugabannin biyu su yi abin da ya dace domin warware wannan matsalar.'' Equatorial Guinea ta juma tana zargin Kamaru da barin 'yan kasarta da wasu 'yan kasashen  Afirka suna shiga iyakokinta ba a kan ka'da ba.