An shiga takon saƙo tsakanin Rasha da Belarusiya game da iskan gas.
June 22, 2010Shugaba ƙasar Belarusiya Alexander Lukashenko, ya bada umurin toshe bututun jigilar iskan Gas daga rasha zuwa Turai mai ratsawa cikin ƙasarsa.Lukashenko ya ɗauki wannan mataki a matsayin martani ga kamfanin Gazprom na ƙasar Rasha bayan ya rage yawan iskan gas ɗin da yake baiwa Belarusiya da kashi 15 cikin 100 kamar yadda shugaban kamfanin Gazprom Alexj Miller ya yi bayani:
" A yau mun yanke shawara rage kashi 15 cikin ɗari na iskan gaz zuwa Belarusiya.Daga yanzu za mu iya bada kashi 85 kawai har sai lokacin da ƙasar ta biya bashin da muka tambayo ta na Euro miliyan 155."
To saidai a cewar sanarwar fadar mulkin Minsk, itama Belarusiya ta tambayo kamfanin gazprom zunzurutun kuɗi Euro miliyan 211 na jigilar gas zuwa Turai.
Ƙungiyar Taraya Turai tayi kira ga ɓangarorin biyu su gaggauta warware wannan taƙƙadama ta hanyar muntunta yarjejeniyar da suka rattabawa hannu.
Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Umaru Aliyu