Rikicin addini a Sokoto
July 19, 2007Talla
A daren jiya ne wasu mutane ɗauke da makamai, su ka kai hari ga wani shehun mallamin sunni a birnin Sokoto dake taraya Nigeria.
Magoyan bayan wannan malami da yayi ƙaurin suna, wajen suka aƙidar Schi´a, na ɗora alhakin wannan aika-aika, ga yan Schi´ar Sokoto.
A game da haka, su ka tada zanga-zanga a wata unguwar yan schi´a , saidai jami´an tsaro su ka tarwarsa su.
Wakilin sashen haussa na DW dake Sokoto wato Aminu Abdullahi, ya yi ƙarin haske a game da faruwar wannan sabuwar fitina.