1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kan iyaka, Soma da Kenya

Abdourahamane Hassane
January 25, 2021

An ba da rahoton cewar an kabsa kazamin fada a kan iyakar Somaliya da Kenya wanda a ciki mutane guda tara suka mutu kana wasu biyu suka jikkata.

https://p.dw.com/p/3oOfH
Somalia Kenianische Soldaten im Kampf gegen gegen Al-Shabaab
Hoto: picture alliance/AP Photo/B. Curtis

Hukumomin Somaliya sun ce sojojin Kenya sun kutsa kai cikin garin Bulohawo a lardin Jubaland domin kai hare-hare a kan dakarun gwamnati, sai dai Kenya ta musunta zargin. Jubaland yanki mai kwarya-kwarya 'yancin gashin kai da ke a kudancin Somaliya kan iyaka da Kenya, ya kasance musababbin rikicin tsakanin makobtan biyu wato Kenya da Somaliya.