1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Iyalan Mandela

July 5, 2013

Gwamanati da sauran al'umma a Afirka ta Kudu na ci gaba da yin kira ga Iyalan Mandela da su sasanta rikicin da ya kunno kai a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/192oI
Hoto: Reuters

Fadar gwamnati a Afirka ta Kudu ta bukaci Iyalan tsohon shugaban kasar Nelson Mandela da su sasanta rikicin da ke tsakaninsu ta hanyar laluma, wanda ya taso a baya-bayannan kan inda za a binne Mandela da a yanzu haka ke kwance a asibiti cikin matsanancin hali na rashin lafiya in rai ya yi halinsa.

Kakakin gwamnatin Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudun Mac Maharaj ne ya yi wannan kira, ya na mai cewa abin takaici ne ace an samu sabani tsakanin iyalan na Mandela a wannan lokaci, inda ya ce akwai bukatar su sasanta rikicin ba tare da bata lokaci ba.

A hannu guda kuma likitoci sun shawarci iyalan na Mandela da ke da shekaru 94 a duniya, da su bari a kashe injin da yake taimaka masa wajen yin numfashi a yanzu haka da yake kwance a asibiti saboda kwakwalwarsa ta daina aiki. Sai dai kuma hukumomin kasar sun musanta batun daina aikin kwakwalwar ta Mandela.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu