1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici Maiduguri na ci gaba da ɗaukar sabon salo

August 15, 2011

'Yan Sanda a Nijeriya sun bayyana kissar mutumin da suka ce yana ƙoƙarin kai harin ƙunar baƙin wake ne

https://p.dw.com/p/12GwP
Wani Caji-ofis a birnin Maiduguri da aka kaiwa hari a ranar 15.06.2011,Hoto: DW

Rundunar 'yan Sandan Najeriya ta sanar da harbe wani mutumin da tace yayi yunƙurin tayar da bam a hedikwatar rundunar dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno ne a wannan Litinin, yini ɗaya kachal gabannin wani kwanitin da shugaban ƙasar ya kafa akan rikicin ƙungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haramun a ƙasar ya miƙa rahoton sa ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

'Yan Sandan suka ce sun yi amannar mutumin yana shirin tada wasu abubuwan da ka iya tarwatsewa ne, waɗanda kuma aka dasa a cikin motar da ɗan ƙunar baƙin waken ke ciki. Mai magana da yawun rundunar 'yan Sandan Abubakar Kabru ya sanar da cewar mutumin ya nufi ginin hedikwatar 'Yan sandan ne, ba tare da nema ko kuma samun izinin shiga harabar hedikwatar rundunar 'yan Sandan ba, bayan buge ƙofar shiga wurin, gabannin jami'ai su harbe shi - har lahira.

Fito-na-fito a tsakanin jami'an tsaro da kuma ƙungiyar nan da aka fi sani da Boko Haramun dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama musamman a birnin na Maiduguri dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar