Rikici a jam'iyar PF ta Zambiya
November 19, 2014Christine Kaseba mai dakin marigayi Sata ta ce za ta tsaya takara duk da ya ke cewa har yanzu yana da matukar wahala ta iya mantawa da tsohon mijin nata da ya rigamu gidan gaskiya makwanni ukun da suka gabata. Kaseba ta ce ta yanke shawarar tsayawa takarar ne domin karasa abubuwan alkhairin da mijinta ya fara gabanin mutuwarsa. Mai shekaru 55 a duniya Kaseba da ke zaman kwararriyar likitar mata ta ce babu wanda ya cancanci ya gaji mijinta sai ita kasancewar ta jima ta na aiki tare da shi, a sabo da haka ita ce za ta iya hada kan jam'iyyarsu ta PF. Sai dai bayyana aniyar tata ya janyo rarrabuwar kai a jam'iyyar ta su ta PF. Shi ma dai dan marigayi Sata, Mulenga Sata da ke zaman magajin garin Lusaka ya bayyana bukatar jam'iyyar ta su ta PF ta tsayar da shi a matsayin dan takararta a zabukan shugaban kasar, yayin da mataimakin ministan kasuwanci da ke zama dan dan uwaa ga marigayi Sata, Miles Sampa ya bayyana bukatar tsayawa takarar a jam'iyyar ta PF.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane