1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a cikin jam´iyar SPD a nan Jamus

November 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvN4

Duk da wani rikici na cikin gida da jam´iyar SPD ta fada ciki bayan sanarwar ajiye aiki da shugabanta Franz Müntefering ya bayar, jam´iyun Christian Union da na ´yan social democrats na ci-gaba da gudanar da shawarwarin kafa wani babban kawance. A tattaunawar da suka yi jiya da daddare wakilan jam´iyun sun shawarta game da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati don cike gibin dubban miliyoyin euro a kasafin kudin kasar ta Jamus. Shugabar jam´iyar CDU kuma shugabar gwamnati mai jiran gado Angeler Merkel da shugaban SPD Müntefering sun nunar a fili cewa za´a ci-gaba da shawarwarin kafa gwamnatin kawance duk da rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin shugabannin SPD game da wanda ya cancanci samun mukamin babban sakataren jam´iyar.