1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimu tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya

Uwai Abubakar Idriss/ SBApril 27, 2016

Wannan matsala dai ta zama wani babban kalubale da ake fuskanta a sassa daban-daban na Najeriya, inda jihohi irin su Katsina ke kokarin shawo kan lamarin.

https://p.dw.com/p/1Idon
Niger Agadez Afrika
Hoto: picture-alliance/Bildagentur-online/Hermes Images

To matsalar ta rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma da ma sauran al’ummar Najeriyar dai, sannu a hankali na ci gaba da watsuwa daga yankin Arewacin Najeriyar zuwa Kudanci da ma Kudu maso Gabashin kasar, inda masu kai hare-hare ke canza salo daga satar shanu ya zuwa ta garkuwa da mutane. Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya su ne suka fi dandana azabar wannan matsalar abin da ya sanya su taron dangi kan lamarin. Alhaji Aminu Bello Masari shi ne gwamnan jihar Katsina da ke jagoranci wannan aiki.

Nigeria - Landwirtschaft bei Katsina
Hoto: AP

"To kashi 80 cikin 100 na mutane sun kai ga koma wa gidajensu, domin daga watan Yunin bara da muka fara, mun samu shanu 15,800 baya ga awaki da jakuna, amma saboda an kashe kasuwar, sai suka bullo da garkuwa da jama’a wasu kuma suka zama ‘yan fashi da makami. Amma wannan ba wai an sa masu ido bane domin abin da ake so a samu cigaba, kuma an samu kashi 80 to sauran kashi 10 da ya rage na wannan matsala, saboda haka kashi goman duk wanda ya yi za’a iya kama shi’’

Nasarar da suka samu ta sanya jihar Katsinan shirin gudanar da taron koli na tattalin arziki da zuba jarri. To sai dai sanin cewa rikicin da gwamnan ke danganta shi da alaka da Boko Haram na daukan sabon salo, inda ake tunanin yin amfani da sulhu maimakon ci gaba da karfin bindiga ta hanyar koyi da jihar Kano da ke koyawa Fulanin sana’o'i. Watsuwar da rikicin na Fulani makiyaya da manoma ke yi, ya sanya karuwar neman mafita musamman na baya-baya nan da ya faru a Enugu, abin da ya sanya shugabannin siyasa shiga lamarin.