Rayuwar Winnie Mandela
April 3, 2018Wasu daga cikin al'ummar kasar na ci gaba da nuna alhini da kuma waiwayen gwagwarmayar da Winnie Mandela ta yi a kokarin samarwa bakar fata a kasar 'yanci da kuma tuni da lokacin da aka sako tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, wanda a lokacin ya ke auren Winnie Madikizela Mandela. A ranar 11 ga watan Fabrairun shekara ta 1990 marigayi Nelson Mandela, rike da hannun marigayiya matarsa Winnie sun zagaya birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, ‘yan sa'o'I da barin gidan yarin da ya kwashi fiye da shekaru ashirin da bakwai a tsare, rike da ita da hannu guda yayin da ya ke daga daya hannun nasa a wata alama ta nasara.
Marigayiyar ta kasance a wancan lokacin daya daga cikin kalilan na bakar fata da ke aikin taimaka wa al'uma a kasar Afirka ta Kudu, gabanin haduwarta da Mista Mandela a shekara ta 1958. Wa ta da ke masaniya kan tarihinta Anne Marie du Prezz Bezdrob, ta bayyana cewa, duk da kasancewar Winnie mai aikin taimaka wa jama'a, ta yi gwagwarmaya a siyasa bil hakki, hakan za a ce ya soma tasiri bayan da ta auri Nelson Mandela.
Amman kuma gwamnatin mulkin farar fata ta wancan zamani, ba ta kyale Winnie da Mandela sun more rayuwa irin ta iyali yadda ya dace ba, saboda kama marigayi Mandela da aka yi a shekara ta 1962, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai. Duk da haka Winnie Mandela ta ci gaba da fadi tashi da kuma kokarin ganin ta reni ‘ya'yanta mata biyu da ta haifa, yayin da ta ci gaba da gwagwarmayar yaki da gwamnatin farar fata ta wariyar launin fata, abinda ya sa mahukunta kama ta, aka kuma yi ma ta daurin kare kukanka na sama da shekara guda, lamarin da ya sa ta zaman kadaici ba tare da ta gani ko magana da wani dan adam ba.
Haka kuma a tsakanin shekara ta 1977 zuwa 1985, sojojin kasar sun tilasta ma ta barin mahaifarta a Soweto, zuwa wani dan karamin kauye da ke bangaren Johannesburg, a shekara ta 1990 da aka sako mijinta Nelson Mandela daga gidan kaso, sai aurenta ya fara tangal-tangal, daga karshe dai suka rabu shekaru biyu da fitowar Mista Mandela daga gidan yari. Winnie ta ci gaba da daukar hankali, duk kuwa da rabuwarta da Mandela. An kuma yi zargin wasu daga cikin 'yan kungiyar kwallon kafar Mandela United da aikata laifukan kisa da fyade, inda nan kuma wani kwamitin bincike, ya sami Winnie da hannu cikin lamarin, amman kuma ta musanta zarge-zargen.
Cikin wasu shekaru bayan nan marigayiya Winnie Mandela ta ci gaba da gudanar da harkokinta gaba-gadi, ba tare da tana la'akari da duk wani kokari na kaskantar da ita da ake yi ba.Tana kuma fitowa fili tana sukar jam'iyya mai mulkin kasar wato ANC. Ta kuma sha sukar tsohon mijin na ta. A yanzu ga talakan kasar Afirka ta Kudu, Winnie Madikizela Mandela, jaruma ce da ta ciri tuta a gwagwarmayar sama masu ‘yanci.