Yanzu haka akwai sama da mutane 5000 dake gudun hijira a kananan hukumomin Faskari da Dandume da ke jihar Katsina sakamakon hare-haren 'yan bindiga. 'Yan gudun hijirar dai sun kunshi mata da kananan Yara. A sansanin 'yan gudun hijirar akwai mata 32 da suka haihu.