1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waiwaye kan rayuwar Mandela ya dauki hankalin Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
July 20, 2018

A ranar 18 ga watan Yuli aka yi bikin tunawa da ranar haihuwar Nelson Mandela wanda da yana raye, a wannan rana ya cika shekaru 100 da haihuwa.

https://p.dw.com/p/31oDz
John Adams Nelson Mandela
Zanen hoton tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson MandelaHoto: picture-alliance/dpa/B. Curtis

A labarin da ta buga mai taken mafarkin Nelson Mandela bai tabbata ba, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa kadan ya rage daga burin Mandela na ganin Afirka ta Kudu ta zama kasa wadda al'ummominta mabambanta za su rayu kafada da kafada ba tare da nuna wariya ba.  Jaridar ta ce Mandela wanda ya yi yakin kawar da mulkin wariyar launin fata da danniya, kuma ya yi zaman kurkuku tsawon shekaru 27, da yana raye da a ranar 18 ga watan Yulin 2018 ya cika shekaru 100 a duniya.

London Mandela Rede 46664 Kampagne
Nelson Mandela tsohon shugaban Afirka ta KuduHoto: Getty Images/S. Barbour

A lokacin da aka sako shi daga kurkuku a 1990 yana da shekaru 72. A 1994 ya zama shugaban kasa, duk da yawan shekarunsa ya yi kokari ya hana bakar fatar kasar daukar fansa a kan danniya da cin zarafi da kuma wariyar da tsiraru farar fata suka nuna musu tsawon shekaru gommai. Akidarsa ta yafiya ta taka rawa wajen samun zaman lafiya a Afirka ta Kudu bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.

Takaita wa'adin mulki don radin kai

Ita ma jarida Neues Deutschland ta leka kasar ta Afirka ta Kudu albarkacin bikin cika shekaru 100 da haihuwar marigayi Nelson Mandela. Ta ce a matsayin shugaban Afirka ta Kudu lokacin da kasar ta rugumin tsarin dimukaradiyya, Mandela ya takaita wa kansa wa'adin mulki guda daya, inda ya mayar da hankali wajen yin sulhu, matakin da jaridar ta ce akwai basira a ciki saboda dimbin kalubale na tashe-tashen hankula da ya kusan jefa kasar cikin yakin basasa. Sai dai rashin daidaito ya rigaya ya samu gindin zama a kasar. Amma jaridar ta ce ba za a taba mantawa da bajinta da yafiya da Mandela ya nuna lokacin mulkinsa ba.

Dambarwa a yankin Ingilishi a Kamaru

Briefe aus dem Gefängnis - Nelson Mandela
Kundin littafi mai kunshe da kasidun Nelson MandelaHoto: DW/J. Carlos

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon tsokaci ta yi a kan rikicin kasar Kamaru tana mai nuni da tantuna da aka kakkafa a bakin tsaunuka inda wasu 'yan kasar ta Kamaru da suka shiga halin ni 'yasu suka samu mafaka. Ta ce tashe-tashen hankula da ake fuskanta da sojoji da rigingimu a yankin Kamaru masu amfani da harshen Ingilishi na kara tilasta wa mutane tserewa daga yankunansu na asali zuwa tarayyar Najeriya. A halin ma da ake ciki Majalisar Dinkin Duniya da gwamnati na fargaba rikicin ka iya bazuwa zuwa kan iyaka. Akwai jita-jitar da ke cewa wasu sojojin Kamaru sun bad da kama sun shiga cikin 'yan gudun hijira, idan kuma suka ci gaba da zama kan iyaka ana iya samun matsalar rashin tsaro.

Sukar lamiri ga kotun ICC

Internationaler Strafgerichtshof in Den Haag ICC
Alkalan kotun duniya da ke HagueHoto: AP

Alkalai na kotun hukunta laifukan yaki ta duniya wato ICC na shan suka musamman daga kasashen Afirka, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da a ranar 17 ga watan Yulin nan aka cika shekara 20 da sanya hannu kan yarjejeniyar da ta assasa kotun ta ICC. Jaridar ta ce a kasashe da dama na Afirka ana nuna rashin gamsuwa da aikin kotun inda ake mata kallon 'yar amshin Shatar Turawan mulkin mallaka, ana kuma zarginta da mayar da hankali kacokan kan Afirka.