1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayukan fararen hula na salwanta a Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
March 1, 2022

Mace-macen fararen hula na karuwa a Ukraine a daidai lokacin da sojojin Rasha ke ci gaba da kai farmaki a wasu manyan birane na kasar. Baya ma mutuwar mutane takwas a birnin Kharkiv, wasu karin biyar sun mutu a Kiev.

https://p.dw.com/p/47q6j
Ukraine Konflikt Russische Invasion Charkiw
Hoto: Marienko Andrew/AP/picture alliance

 Rahotannin sun nunar da cewa akalla mutane takwas sun mutu yayin da shida suka jikkata a birnin Kharkiv da ke gabashin Ukraine, sakamakon wani hari da jiragen yakin Rasha suka kai. Yayin da hukumar ba da agajin gaggawa ta Ukraine ta ce mutane biyar sun mutu yayin da biyar suka jikkata a wani harin da Rasha ta kai kan hasumiyar tashar talabijin gwamnati da ke Kiev babban birni.

Ita dai Rasha ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a Ukraine har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi, inda ta tura motocin sulke, da makamai atilari domin kewaye biranen Kiev da Kharkiv da Odessa da Kherson da Mariupol da nufin mayar da su karkashin ikonta.  Sai dai 'yan Ukraine na nuna turjiya musamman ma a Kiev babban birni kasar sakamakon makamakai da suke samu daga kasashen yammacin duniya. Ana sa ran rikicin na Ukraine ya mamaye jawabi na farko da Shugaba Joe biden na Amirka zai yi a majalisar kasarsa.

Majalisar Dinkin Duniya da kawancenta sun kaddamar da kira na gaggawa domin a tara dala miliyan 1,700 da nufin samar da agajin jin kai da Ukraine ke bukata bayan da Rasha ta mamaye ta.