Rayuka sun salwanta a Saliyo
August 15, 2017A halin da ake ciki ma'aikatan ceto sun tono gawarwaki kimanin 270 daga ibtila'in na zaftarewar laka da ya faru a wajen babban birnin kasar Saliyo wato Freetown da sanyin safiyar ranar Litinin. Chernor M Barrie shi ne jami'in kula da aikin ceto na kungiyar agaji ta Red Cross ya ce yanzu haka ma'aikatansu sun bazu a lungu da sako na unguwannin da lamarin ya fi muni. "Yanzu aiki ne na gano maimakon na ceto. Akwai mutane da muka ceto amma yawansu bai taka kara ya karya ba, mun kuma ba su agajin farko. Da taimakon rundunar soji da kungiyar Red Cross da 'Yan kwana-kwana da sauran kungiyoyi, mun kwashe mutanen zuwa aibiti."
Gwamnati dai ta yi alkawarin ba da kayan agaji ga mutane fiye da 3000 da suka rasa gidajensu, inda yanzu haka ta bude wata cibiyar ba da taimakon gaggawa a unguwar Regent da ke kan tsauni, sannan za a bude wasu cibiyoyin rajistar wadanda suka rasa gidajensu a wurare da dama da ke birnin Freetown mai yawan mutane kimanin miliyan daya. A jawabin da ya yi wa al'ummar kasa a ranar Litinin, shugaba kasar Ernest Bai Koroma ya yi kira da hadin kan 'yan kasar ta Saliyo da har yanzu ke gwagwarmayar daidaita al'amura bayan annobar cutar Ebola da kuma yakin basasan da ta yi fama da shi a shekarun baya.
"Na damu da wannan bala'i da ya afka wa kasarmu. Ina mai mika ta'aziyata ga dukkan iyalen da ke cikin makoki sakamakon wannan bala'i da ya shafi dukkan 'yan kasar nan baki daya. Ku bari mu yi amfani da wannan lokaci mu hada kai, mu yi wa juna jaje kana kuma mu taimaki juna." Shugaban dai ya yi kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu kana su guji zuwa wurare masu hatsari a dai dai lokacin da ake kokarin shawo kan halin da ake ciki. Ya ce gwamnatinsa na hadin gwiwar da kawayenta masu ba da agaji inda tuni aka kafa cibiyar ba da agajin gaggawa.