Najeriya: Rashin mutumta hakkin dan Adam
June 23, 2023Kungiyar ta HRMI da ke Swithzerland ta yi bincike mai zurfi a kan abubuwa da dama da dukkansu hakkoki ne da ya kamata gwamnati ta bai wa 'yan kasa, ba wai kawai batu na musgunawa ko gana azaba ba har ma da hakkin kula da lafiyarsu da samar musu da abinci da muhalli da ma aikin yi. Cibiyar auna mizanin kare hakkin dan Adam din ta HRMI da ke Switzerland ta bayyana cewa, halin da kare wadanan hakoki ke ciki a Najeriyar ya yi muni fiye da na sauran kasashen da ke yankin Kudu da Saharar Afirka. Nazarin da cibiyar ta fitar ya nuna cewa fannin samar da ilimi a Najeriyar, shi ne ya fi fuskantar koma-bayan sosai. An fitar da wannan rahoto ne a daidai lokacin da Najeriyar ke kara zama abin sha'awa ga kasashe da dama, inda suke ta yaba matakan farko da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya dauka bayan darewa kan mulki. Batun kula da kare hakkin dan Adam a Najeriyar dai, lamari ne da ya dade yana fuskantar kwan-gaba kwan-baya a cikin kasar.